Ƙungiyar Ambassador Yusuf Tuggar Foundation ta yi watsi da ikirarin cewa tsohon gwamnan Jihar Bauchi, Mohammed Abubakar, shi ne ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
Sakataren ƙungiyar, Shehu Ningi, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata a Bauchi.
Yusuf Tuggar, tsohon Ministan Harkokin Wajen Najeriya, ya sha kaye a ƙoƙarinsa na samun tikitin takarar gwamna na APC a zaɓen fidda gwani da aka gudanar a watan Mayu.
Shugaban kwamitin gudanar da zaɓen fidda gwani na APC, John Abang, ya sanar da cewa Mohammed Abubakar ne ya yi nasara bayan ya doke Yusuf Tuggar da sauran masu neman takara biyar.
Sakamakon da aka bayyana ya nuna cewa:
Mohammed Abubakar ya samu ƙuri’u 57,517.
Yusuf Tuggar ya samu 26,001.
Bala Wunti ya samu 13,648.
Sauran masu neman takarar sun haɗa da:
Nura Soro – 13,638
Kabir Ma’aji – 8,157
Baba Suleiman – 7,688
Yakubu Abdullahi – 7,181
Sai dai Shehu Ningi ya yi watsi da sanarwar, yana mai cewa ba a gudanar da sahihin zaɓen fidda gwamna a jihar Bauchi ba.
A cewarsa:
“Mun kira wannan sanarwa ne saboda Mohammed Abubakar ne da kansa ya ayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara, ba tare da wata sanarwa ta hukuma daga jam’iyyar APC ba. Wannan abu ne da ba a saba gani ba.”
Ya ƙara da cewa har zuwa yanzu jam’iyyar APC ba ta fito fili ta tabbatar da wannan sanarwa a hukumance ba, sai dai shirunta ya sa wasu ke ganin kamar ta amince da ikirarin.
Ningi ya bayyana cewa ƙorafin da suka shigar ya ta’allaka ne kan muhimman batutuwa guda huɗu:
1. Rashin gudanar da zaɓen fidda gwamna.
2. Illar da hakan ka iya haifar wa jam’iyyar APC.
3. Saɓanin bayanai kan yadda aka ayyana Mohammed Abubakar a matsayin ɗan takara.
4. Muhimmancin adalci da tsarin karɓa-karɓa (rotation) wajen rabon mulki.
A ƙarshe, ya buƙaci shugabannin APC da su sake duba lamarin bisa adalci, gaskiya, dimokuraɗiyya ta cikin gida da kuma muradun jam’iyyar domin ta samu damar yin nasara a zaɓe a jihar Bauchi.
