Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da samun mutane 105 da ake zargin sun kamu da cutar sankarau a ƙananan hukumomi 20 na jihar, sakamakon tsananin zafin da ake fama da shi a yankunan su.
Babban Daraktan Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Katsina, Dakta Shamsuddeen Yahaya ne, ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai.
Ya ce har yanzu zargin mutanen ake na ɗauke da cutar bisa nuna wasu alamomi da ake kokarin tabbatarwa ta hanyar gwaje-gwaje.
Ya ƙara da cewa duk wanda ya nuna alamomin cutar kamar matsanancin ciwon kai da sankarewar wuya a gaggauta ba shi kulawar lafiya tare da sanya ido a kansa.
Dr Shamsuddeen ya bayyana cewa, wasu ƙananan hukumomi sun fi nuna alamomin cutar sama da wasu, yana mai cewa gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen sa ido da ɗaukar matakan gaggawa domin daƙile yaɗuwar cutar ta sankarau.
Ya kuma bayyana cewa an ƙaddamar da Cibiyar Ayyukan Gaggawa domin haɗa kai da ma’aikatan lafiya wajen aiwatar da matakan daƙile cutar a faɗin jihar.
