Shugaban jam’iyyar APC a Kano, Umar Haruna Doguwa, ya yi alƙawarin sauke duk wani shugaban jam’iyyar da ke Kano ta Kudu da aka samu ya sayar da motar ko babur ɗin da Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila ya ba shi.
Doguwa ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen taron rabon tallafi ga al’ummar ƙananan hukumomi 16 na Kano ta Kudu da Sanata Kawu Sumaila ke wakilta.
Ya ce motocin ƙirar Sharon guda 16 da aka bai wa shugabannin APC na yankin, tare da babura 400 da aka raba wa masu ruwa da tsaki da kekunan ɗinki 450 ga ’ya’yan jam’iyyar, an samar da su ne domin ƙarfafa ayyukan jam’iyyar da bunƙasa tattalin arzikin al’umma.
Shugaban jam’iyyar ya jaddada cewa kayan tallafin ba na sayarwa ba ne, yana mai cewa an bayar da su ne domin sauƙaƙa ayyukan jam’iyyar da taimaka wa waɗanda suka amfana da su wajen dogaro da kai, tare da rage fatara da talauci a yankin.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Doguwa na gargaɗin shugabannin jam’iyyar da su tabbatar sun yi amfani da kayan tallafin bisa manufar da aka samar da su, yana mai cewa ba zai lamunci duk wanda ya karkatar da su ko ya sayar da su ba.
