An gano gawar wani matashi mai suna Sani Karami, wanda ya ɓace tun ranar Asabar, a cikin ruwan da ke ƙarƙashin gadar Ɗan’agundi a jihar Kano.
Kanin mahaifiyar matashin, Malam Sa’ad Uba Kwalli, ne ya bayyana hakan, inda ya ce iyalan marigayin sun shafe kwanaki suna nemansa bayan ɓacewarsa.
A cewarsa, tun ranar Asabar suke neman Sani Karami ba tare da samun wani bayani kan inda yake ba, har sai ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2026, lokacin da suka samu labarin cewa an hangi gawarsa a ruwan Ɗan’agundi.
Bayan samun rahoton, jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano sun isa wurin domin gudanar da aikin tsamo gawar daga ruwan.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a tabbatar da kammala aikin tsamo gawar ba.
Malam Sa’ad ya kuma bayyana cewa Sani Karami ba ya shaye-shaye, yayin da iyalansa ke jiran ƙarin bayani kan abin da ya faru da shi.
Har yanzu ba a tabbatar da musabbabin mutuwar matashin ko yadda ya faɗa cikin ruwan ba.
