Majalisar ɗinkin duniya ta bayyana cewa kimanin ‘yan Najeriya miliyan 35 na fuskantar barazanar matsananciyar yunwa daga watan Yuni zuwa Agusta na shekarar 2026.
A wata sanarwa da Ƙungiyar Agajin Gaggawa ta UN ta fitar a birnin New York, ta ce matsalar ƙarancin abinci na ƙara tsananta a Najeriya musamman yayin da lokacin ƙarancin abinci ke gabatowa.
Rahoton ya nuna cewa kusan mutum ɗaya cikin bakwai a Najeriya na iya shiga matsananciyar yunwa, inda aka fi fama da matsalar a jihohin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.
Majalisar ta kuma ce yara miliyan 6.4 a yankunan biyu na iya fuskantar matsanancin rashin abinci mai gina jiki a bana.
Ƙungiyar ta yi kira ga ƙasashen duniya da su bayar da tallafin gaggawa, tana mai cewa idan ba’a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, iyalai da dama za su rage yawan abincin da suke ci, sayar da kadarorinsu ko kuma cire ‘ya’yansu daga makarantu.
Rahoton ya ƙara da cewa shirin bayar da agajin jin ƙai na dala miliyan 516 da aka tsara a shekarar 2026 ya samu kaso 40 cikin 100 kacal na kuɗaɗen da ake buƙata, inda aka tara dala miliyan 215 zuwa watan Mayu.
