Batun jinkirin zaben sabon mataimakin gwamnan Kano na ci gaba da zama batun tattaunawa da muhawara.
Masana siyasa sun bayyana gazawar shugabannin siyasa, a matsayin abin da ya kawo tsaiko wajan zabar sabon mataimakin gwamnan Kano.
Tsawon makonni 3 kenan zuwa yanzu jihar Kano bata da mataimakin gwamna, tun bayan murabus din Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo.
Dakta Sai’du Ahmad Dukawa, mai sharhi kan harkokin siyasa a kasarnan, ya ce zabar sabon mataimakin gwamnan, babu wata matsala da zai haifar idan an bi hanyoyin da kowanne bangare ya gamsu.
