Majalisar Kolin Shari’ar Addinin Muslunci ta kasa ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ta bukaci Musulmai da su gudanar da addu’o’i domin a cire Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC Joash Amupitan.
A cikin wata sanarwa da Babban Sakatarenta, Nafiu Baba Ahmad, ya fitar a ranar Litinin, majalisar ta bayyana zargin a matsayin ƙarya, sannan kuma marar tushe.
Majalisar ta ce ba ta taba bayar da irin wannan umarni ba, tare da kira ga jama’a, musamman al’ummar Musulmi da kuma kafafen yada labarai, da su yi watsi da wadannan rahotanni, su dogara kawai da hanyoyin sadarwar hukumar majalisar.
Majalisar ta nesanta kanta daga ikirarin yin addu’ar, ta kuma sake jaddada matsayarta ta baya, kan Shugaban INEC, inda ta ta ke cewa ba shi da wani tasiri da ake bukata a mukaminsa, kuma ya kamata ya yi murabus ko a cire shi.
A cewar majalisar, matsayarta ta samo asali ne daga damuwa kan wasu ayyuka da halaye da take ganin suna nuna son kai a kan Musulunci da Musulmi.
