A yau Talata Jam’iyar ADC ke gudanar da babban taronta na kasa a zauren taron na Rainbow Suite dake Abuja.
Tuni dai mambobin jam’iyar daga sassa daban daban na kasar nan suka mamaye gurin taron.
Wannan na zuwa ne yayin da ADC ke fama da rikicin shugabanci tsakanin bangaren shugabancin David Mark da Nafiu Bala.
Ana sa ran dubban wakilan jam’iyyar za su halarci taron, inda za a tabbatar da sabon shugabancin jam’iyyar ƙarƙashin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark.
Taron na ADC na zuwa ne a ranar da ake jiran hukuncin kotu kan rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar.
Dangane da yadda taron ke gudana mun tattauna da wakilin mu Suhaib Auwal Gwagwarwa, da ke cen Abujan ya yi mana karin bayani kan halin da ake ciki a harabar gurin taron.
Itama shugabar kungiyar mata ‘yan jarida na ADC Hannatu Sulaiman Abba ga karin bayanin da ta yi mana.
a a iya tunawa jam’iyyar ADC ta shiga tsaka mai wuya bayan ƙarar da ɓangaren tsohon mataimakin shugabanta na ƙasa, Nafiu Bala Gombe, ya shigar yana ƙalubalantar halaccin shugabancin David Mark.
Haka kuma Hukumar Zaɓe INEC ta cire sunan shugabancin ɓangaren David Mark a shafinta, bisa hujjar abin da ta Kira umarnin kotu na cewa a koma yadda al’amuran jam’iyyar suke a baya.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da bibibiyar halin da ake ciki har zuwa hukuncin ƙrashe da kotu za ta yanke kan shugabancin jam’iyyar.
