Shugaban yayi ganawar ne bayan harin soji a kasuwar Jilli dake iyakar Borno da Yobe wanda rahotanni suka ce ya hallaka akalla mutane 200, yayin da wasu da dama suka jikkata. Ganawar da aka yi jiya Litinin na zuwa ne bayan dawowar shugaba Tinubu daga ziyarar da kai jihohin Lagos, Ogun da Plateau.
Cikin wadanda shgaban ya gana da su akwai Mai bawa shugaban kasa shawara kan tsaro Mallam Nuhu Ribadu da babban hafsan tsaro da hafsan sojin kasa, da na sama da daraktan hukumar DSS da babban sufetan yan sanda na kasa. A ranar Asabar ne wani harin jirgin yaƙi ya kashe mutanen da suka je cin kasuwar Jilli da ke kan iyakar jihohin Borno da Yobe dake Arewa maso gabashin kasar nan.
Sai dai sojojin sun ce sun kai harin ne kan da nufin farwa mayaƙan Boko Haram da ke yankin, amma ba ta yi niyyar kaiwa farar hula hari ba.
