Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya gargadi masu kokarin siyasantar da matsalar tsaro, yana mai cewa ba za a lamunci hakan ba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron Majalisar Tsaron Jihar, inda aka duba halin tsaro da matakan da ake dauka domin kare rayuka da dukiyoyi.
Gwamnan ya ce ba za a lamunci duk wani yunkuri na juya matsalar tsaro zuwa siyasa ba, musamman a wannan lokaci na siyasa.
Ya kuma jaddada kudurin gwamnatinsa na ci gaba da daukar matakan da za su tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.
