Hukumar kula da kotunan jihar Kano ta musanta labarin da ake yadawa cewar babbar kotun Kano ta wanke Murtala Sule Garo daga dukkanin badakalar cin hanci da rashawa.
Kakakin kotunan Kano Baba jibo Ibrahim ne ya bayyana hakan cikin wani sakon murya da ya aikowa premier radio a yau Talata.
Baba Jibo ya ce babu wata kotu da ta zauna tsakanin jiya zuwa yau da ta saurari karar,inda ya bukaci al’umma su yi watsi da wannan batun.
A safiyar yau ne dai wasu rahotanni ke cewa wata kotu a Kano ta wanke tsohon Kwamishinan Kananan Hukumomin, Murtala Sule Garo daga Zargin Rashawa.
