Gwamnatin Tarayyar ta sanar da cewa karfin wutar lantarki ya karu a kasar nan bayan shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya fitar da naira Tiriliyan 3 a bangaren.
An samu ƙaruwa a yawan wutar lantarki da ake samarwa a ƙasar, inda ya tashi daga megawatt 3,951 zuwa megawatt 4,300.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a birnin Abuja, ta bakin Mai Ba Ministan Wutar Lantarki Shawara na Musamman kan Harkokin Sadarwa da Hulɗa da Kafafen Yaɗa Labarai, Bolaji Tunji.
Sai dai duk da wannan cigaba, ‘yan Najeriya da dama na ci gaba da nuna damuwa kan yawaitar katsewar wuta a sassa daban-daban na ƙasar, lamarin da ke shafar rayuwar yau da kullum da harkokin kasuwanci.
