Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya buƙaci a sauya alkalin babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna wanda ke sauraron shari’ar da ake yi a kansa.
Rahotanni sun bayyana cewa El-Rufa’i ya gabatar da wannan buƙata ne ta hannun lauyoyinsa, inda ya nuna rashin gamsuwa da yadda alkalin ke tafiyar da shari’ar.
A cewarsa, akwai dalilan da ke sa ya ke ganin cewa ba zai samu cikakken adalci ba idan aka bar shari’ar a hannun alkalin na yanzu.
A cikin takardun da aka miƙa wa kotu, an roƙi a cire alkalin daga shari’ar tare da miƙa ta ga wani alkalin daban domin tabbatar da gaskiya da adalci.
Lauyoyin El-Rufa’i sun jaddada cewa wannan mataki yana da muhimmanci wajen kare haƙƙinsa na samun shari’a mai adalci ba tare da nuna son kai ba.
Sai dai har yanzu kotu ba ta yanke hukunci kan wannan buƙata ba, yayin da ake sa ran za a ci gaba da sauraron ƙarar bayan an tantance ƙorafin da aka gabatar.
