An sake samun saɓani kan ci gaba da bayar da lasisin shigo da man fetur daga ƙasashen waje, inda masu ruwa da tsaki a fannin ke bayyana ra’ayoyi mabambanta kan matakin da Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA) ke ɗauka.
Ƙungiyar Masu Kasuwancin Man Fetur ta Ƙasa (DAPPMAN) ta kare matakin hukumar na ci gaba da bayar da lasisin shigo da mai, tana mai cewa hakan ya yi daidai da tanadin Dokar Masana’antar Man Fetur (PIA).
Ƙungiyar ta bayyana cewa manufar bayar da lasisin ita ce tabbatar da wadataccen man fetur a faɗin ƙasar tare da kare tsaron samar da makamashi, musamman a lokutan da ake buƙatar ƙarin wadatar mai.
Sai dai wasu masu ruwa da tsaki a fannin sun nuna damuwa cewa ci gaba da shigo da mai daga ƙasashen waje na iya rage ƙwarin gwiwar masu zuba jari a harkar tace mai a cikin gida.
Sun yi nuni da cewa matakin na iya shafar matatar Dangote, wadda ta sha bayyana adawarta ga ci gaba da bayar da lasisin shigo da mai, tana mai cewa hakan ya saɓa da manufar gwamnati ta bunƙasa tace mai a cikin gida da kuma rage dogaro da shigo da man fetur daga ƙasashen waje.
