An shiga firgici a wajen Fadar White House da ke birnin Washington bayan da aka ji karar harbe-harbe da dama a yammacin ranar Asabar, lamarin da ya sa jami’an tsaro da ‘yan jarida da sauran mutanen da ke wurin suka nemi mafaka cikin gaggawa.
Kamar yadda jaridar New York Post ta ruwaito, jami’an hukumar tsaron shugaban Amurka sun umarci ‘yan jarida da su nemi mafaka a filin arewacin fadar kafin daga bisani su garzaya zuwa dakin taron manema labarai da misalin karfe 6:30 na yamma.
Rahotanni sun ce an sanya fadar cikin yanayin kulle saboda lamarin.
Bayanai sun nuna cewa an ji karar harbe-harben ne kasa da sa’o’i biyu bayan Shugaban Amurka, Donald Trump, ya wallafa a shafinsa na Truth Social cewa yana cikin Ofishin Oval yana aiki kan wata yarjejeniyar zaman lafiya da Iran.
