Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB) ta sanar da cewa daga shekarar 2027 za ta baiwa dalibai damar amfani da kwamfutocinsu na kashin kansu wajen rubuta jarabawar UTME.
Magatakardar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ne ya bayyana hakan yayin taron manufofin daukar dalibai zuwa manyan makarantu na shekarar 2026 da aka gudanar a Abuja.
Oloyede ya ce za a sanya na’urar “flash drive” a cikin kwamfutocin domin hana magudi yayin gudanar da jarabawar.
Ya bayyana cewa sabon tsarin zai rage kashe kudi tare da saukaka gudanar da jarabawar, sannan zai magance korafe-korafen da dalibai ke yi kan matsalar mutuwar kwamfuta yayin rubuta jarabawa.
A cewarsa, an tsara wannan mataki ne domin saukaka wa dalibai tare da tabbatar da ingancin jarabawar.
Ya kuma kara da cewa JAMB na shirin bullo da wasu sabbin tsare-tsare nan da shekarar 2027 domin inganta gudanar da jarabawar gaba daya.
Dangane da sakamakon UTME na shekarar 2026, Oloyede ya ce Jesudunsin Owoeye daga jihar Ekiti ce ta zama dalibar da ta fi kowa maki bayan ta samu maki 372 cikin 400 a jarabawar da ta rubuta a jihar Ogun.
Ya ce Owoeye ta zabi Jami’ar Legas a matsayin zabinta na farko domin karantar fannin Likitanci da Tiyata.
Haka kuma, Ikenna Enwere daga jihar Imo ya zo na biyu da maki 370, yayin da Ayomide Bamisile daga jihar Ondo ya zo na uku da maki 369.
