Kimanin alhazan Ummara 4,000 daga ƙasar Indiya ne suka makale a biranen Makka da Madina, bayan soke jiragen da za su mayar da su gida sakamakon ƙarin tsamin dangantaka a yankin.
Alhazan sun je Saudiyya ne ta jiragen kamfanonin IndiGo, Akasa Air da Air India, amma sun kasa komawa ƙasarsu bayan kamfanonin sun dakatar da wasu zirga-zirgar jiragensu zuwa biranen Saudiyya.
Shugaban jam’iyyar AIMIM a Indiya, Asaduddin Owaisi, ya buƙaci gwamnatin ƙasar da Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama (DGCA) da su ɗauki matakin gaggawa domin dawo da alhazan gida.
A wani saƙo da ya wallafa a shafin X, Owaisi ya ce dole ne a samar da mafita cikin gaggawa, domin alhazan da suka je gudanar da ibadar Ummara sun tsinci kansu cikin mawuyacin hali sakamakon soke jiragen.
Ya kuma roƙi hukumar DGCA da ta bai wa kamfanonin izinin amfani da manyan jiragen sama masu ɗaukar fasinjoji da yawa, ko kuma ta shirya jirage na musamman domin dawo da su zuwa Indiya.
