A yau Talata ne ake sa ran kammala taron shugabannin Afirka da Faransa da ake gudanarwa a birnin Nairobi na ƙasar Kenya, inda ake sa ran shugabannin ƙasashe sama da 30 za su rattaba hannu kan yarjejeniyoyin zuba jari da haɗin gwiwa.
An gudanar da taron mai taken “Africa Forward Summit” a cibiyar taruka ta Kenyatta International Convention Centre, ƙarƙashin jagorancin shugaban Kenya, William Ruto, da shugaban Faransa, Emmanuel Macron.
Ga wasu daga cikin manyan batutuwan da suka ɗauki hankali a taron:
Macron ya tsawata wa dalibai
Ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi jan hankali shi ne lokacin da Shugaba Macron ya dakatar da jawabinsa yayin wata ganawa da matasa a Jami’ar Nairobi saboda hayaniyar da wasu dalibai suka rika yi.
“Wannan rashin mutunci ne,” in ji Macron, kafin ya bukaci wadanda ba za su saurara ba su fice daga wajen taron.
Batun bashin Afirka da zuba jari
Shugabannin Afirka sun yi kira ga Faransa da sauran ƙasashen duniya da su sake duba tsarin bada rance ga ƙasashen Afirka, musamman batun yawan kuɗin ruwa.
Sun ce tsarin na yanzu yana ƙara wa nahiyar matsin tattalin arziki.
A nasa bangaren, Macron ya ce zai yi ƙoƙarin ganin an samar wa ƙasashen Afirka damar samun rance mai sauƙin biya, musamman a matsayinsa na shugaban ƙungiyar G7 na bana.
Tinubu ya halarci taron
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya isa Nairobi a daren Litinin domin halartar taron.
Ana sa ran zai gana da shugabanni da ‘yan kasuwa daga Afirka da Faransa kan batutuwan makamashi, fasaha da ababen more rayuwa.
Bayan kammala taron, shugaban zai wuce ƙasar Rwanda domin halartar taron Africa CEO Forum.
Sabon salon Faransa a Afirka
Taron na bana shi ne karo na farko da Faransa ke shirya irin wannan babban taro a ƙasa mai amfani da harshen Turanci.
Macron ya ce ƙasarsa tana son gina “huldar daidaito” da ƙasashen Afirka, musamman bayan janye sojojin Faransa daga wasu ƙasashen Yammacin Afirka.
Haka kuma gwamnatin Faransa ta sanar da sabon tsarin mayar da kayayyakin tarihi da aka kwashe daga Afirka a lokacin mulkin mallaka.
Ana sa ran taron zai ƙare da fitar da sanarwar ƙarshe tare da rattaba hannu kan yarjejeniyoyin zuba jari tsakanin Faransa da ƙasashen Afirka da suka halarta.
