Kasar China ta bayyana tsananin adawarta da takunkumin da Amurka ta ƙaƙabawa wasu kamfanonin ƙasar uku, waɗanda Washington ke zargi da taimakawa ayyukan sojin Iran, in da tace matakin haramtacce ne mai cike da bangarenci.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China, Guo Jiaqun, a wani taron manema labarai yace China ta kan buƙaci kamfanoninta su gudanar da harkokinsu bisa doka da ƙa’ida, kuma za ta kare hakkoki da muradun halastattun kamfanoninta.
Ya ƙara da cewa babban abin da ya kamata a bai wa fifiko shi ne hana sake barkewar rikici ta kowace hanya, ba amfani da yaki wajen danganta wasu kasashe da zargi ko bata suna ba.
