Gomman masunta ne ake gargabar sun mutu bayan hare-hare ta sama da sojojin Chadi suka kai wuraren mayaƙan Boko Haram a yankin tafkin Chadi, a cewar wani shugaban ƙungiyar masunta.
Hare-haren sun faru ne kwanaki bayan da Boko Haram ta ƙaddamar da hare-hare biyu kan sansanin sojin Chadi da ke kusa da tafkin, abin da rahotanni ke cewa ya yi sanadin mutuwar aƙalla sojoji 24 da wasu manyan janar biyu.
Shugaban ƙungiyar masunta ƴan Najeriya a yankin, Abubakar Gamandi Usman, ya shaida wa BBC cewa lamarin ya rutsa da farar hula da dama saboda mayaƙan Boko Haram sun daɗe suna aiwatar da miyagun laifuka a Tafkin Chadi.
A wata sanarwa da aka wallafa a shafukan sada zumunta, Fadar Shugaban Chadi ta ce sojojinta sun kai hare-hare kan cibiyoyin Boko Haram a Tafkin Chadi a matsayin martani kan hare-haren ranar 4 da 6 ga watan Mayu.
Wannan ba shi ne karon farko da ayyukan sojojin Chadi a yankin ke janyo zarge-zargen kisan farar hula ba.
A Oktoban 2024, an zargi rundunar sojin Chadi da kashe masunta ƴan Najeriya da dama a wasu hare-hare ta sama da aka kai kan mayaƙan Boko Haram a tsibirin Tilma da ke Tafkin Chadi.
