Saurari premier Radio
37.5 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiLabaran KanoAbba Kyari ya musanta ta'ammali da miyagun kwayoyi

Abba Kyari ya musanta ta’ammali da miyagun kwayoyi

Date:

Abba Kyari  jami’in ‘dan sandan da aka dakatar ya musanta zargin alakanta shi da kungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ta ƙasa da ƙasa.

An kama Abba Kyari ne a makon da ya gabata bayan da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA ta zarge shi da alaƙa da wata kungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi da ke aiki tsakanin Najeriya da Habasha da kuma Brazil.

Sai dai a ranar Litinin ya shaidawa wata kotu a Abuja  ta hannun lauyoyinsa cewa ƙirƙirar zargin aka yi.

Hukumar NDLEA ta yi zargin cewa Mista Kyari ya yi yunkurin bai wa jami’anta cin hanci  kilo 25 na hodar ibilis da jami’ansa suka kama sannan suka raba, sai dai ya musanta zargin.

Ya ce jami’an hukumar NDLEA ne suka masa gadar zare bayan ya nace sai an bayar da lada ga wanda ya bayar da labarin da ya kai ga kama waɗanda ake zargi da safarar miyagun kwayoyi kamar yadda suka amince da farko.

Ɗaya daga cikin lauyoyinsa Hamza Nuhu Dantani, yace sun kuma gabatar da bukatar neman belinsa.

Ya ce saboda an ci gaba da tsare shi sama da sa’a 24 ba tare da gabatar da shi kotu ba kan zargin da ake masa, wanda ya saɓa ƴancinsa na ɗan adam.

A ranar Alhamis kotu za ta saurari buƙatar da lauyoyinsa suka shigar na neman beli.

Latest stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...

Related stories

Uba Ya Bukaci Kotu Ta Daure Dansa Har Abada A Kano

Wani mahaifi ya yi karar dansa a gaban Kotun...

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...