24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiKwankwaso zai kaddamar da sabuwar kungiya

Kwankwaso zai kaddamar da sabuwar kungiya

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

A yau ake sa ran tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso da wasu muhimman ‘yan siyasa a kasar nan za su kafa sabuwar kungiya da suka kira ta da wadda za ta ciyar da kasar nan gaba.

Za a kaddamar da Kungiyar mai suna The Natonal Movement (TNM) ne a yau Talata a birnin tarayya Abuja.

A na sa ran yayin taron za a fito da manufofin kafa kungiyar da kuma me za ta yiwa jama’a da zarar an samar da ita.

Sai dai ba kamar yadda wasu suka fuskanci batun ba na cewar Kwankwason da wasu fitattun mutane za su kafa jam’iyyar Siyasa ne.

A zantawar Premier Radio da jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar PDP a Kano Bashir Sanata ya ce ko kadan jama’a basu fahinci manufarba.

A cewarsa ba jam’iyyar siyasace za a kafa ba illa, wata kungiya da za ta samar da yan kishin kasa da za su ceto kasar nan daga halin da take ciki.

“Ba jam’iyyar siyasa za a kafa ba, kungiya ce ta ci gaban al’umma da wasu masu kishin kasa suka taru suka samar.

A yanzu dai al’umma na dakon sakamakon taron da za gudanar a yau da zai bayyana makomar Kwankwaso.

Latest stories