Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAbinda yan 'Boko Haram' suka fadamin a 2011-Obasanjo

Abinda yan ‘Boko Haram’ suka fadamin a 2011-Obasanjo

Date:

Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo,ya bayyana abin da ’yan kungiyar Boko Haram suka fada masa lokacin da ya hadu da su a Maiduguri a 2011.

Obasanjo ya bayyana hakan ne ranar Litinin lokacin da yake jawabi ta intanet, a taron Gidauniyar Tunawa da Murtala Muhammad (MMF) mai taken, “Magance ta’addancin Boko Haram, tayar da kayar baya da garkuwa da mutane a Najeriya”.

Obasanjo ya alakanta matsalar tsaron da ake fama da ita yanzu da bazuwar makamai bayan yakin basasar Najeriya.

Ya ce, “Babu inda za mu je matukar ba mu dauki aikin gina kasa da muhimmanci ba ta hanyar kamanta adalci da gaskiya. Dole mu gina kasar da kowa zai zama yana da ruwa da tsaki a cikinta.

“Matsalar tsaron da ake fama da ita a yanzu haka ta samo asali ne daga yaduwar makaman da muka gaza magancewa tsawon lokaci. Kullum lamarin sai kara tabarbarewa yake.

“A shekarar 2011, lokacin da Boko Haram ta fara nuna munanan illolinta, na niki gari na tafi har Maiduguri don na fahimce su, na gano me suke nema.

“Baya ga neman kafa Shari’ar Musulunci, sun kuma yi korafin cewa mambobinsu ba su da ayyukan yi, a daidai lokacin da kuma suke kokarin nema wa kansu halastattun ayyukan, sai gwamnati ta fara bin su tana harbewa.

“Babban abin da na rika jin tsoro a lokacin shi ya ci gaba da faruwa. A lokacin, Boko Haram ba ta da goyon baya daga waje, sai dai kawai ’yan Najeriya da ke da kadarori a waje da ke tallafa musu,” inji tsohon Shugaban Kasar.

Obasanjo ya kuma yi kira ga tsofaffin ’yan siyasar kasar nan da su ja jiki su ba matasa dama don su kai kasar ga tudun mun tsira.

Ya ce kamata ya yi dattawa su hada gwiwa da matasa ta hanyar ba su shawarwari da hikimomi wajen sauya Najeriya.

“Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi ya ce yana Firamare lokacin da ni da Murtala muka shugabanci Najeriya. To ka ga matukar aka ce mutane irin na wancan lokacin za su rika kokawar mukamai da su Fayemi a matsayinsa na Gwamna, ai akwai matsala ke nan,” inji Obasanjo.

Latest stories

Related stories