Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC ta dage babban taronta na kasa

Yanzu-Yanzu: Jam’iyyar APC ta dage babban taronta na kasa

Date:

Jam’iyyar APC  ta sake dage ranar gudanar da babban taronta na kasa har sai abin da hali ya yi.

Wannan dai na zuwa ne a sakamakon rikicin cikin gida da jam’iyyar take fuskanta a wasu sassanta bayan ta tsayar da ranar 26 ga watan Fabrairu tun da farko.

Jam’iyyar APC ta sanar da dage taronta a cikin wata takarda da ta aika wa Hukumar Zabe ta Kasa INEC mai dauke da sa hannun shugabanta na riko, Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe.

“Muna sanar da Hukumar Zabe cewa jam’iyyarmu ta yanke shawarar gudanar da zaben shiyoyi a ranar Asabar 26 ga watan Maris.”

Hakan na nufin an dage taron tsawon wata daya.

Ya zuwa yanzu dai jam’iyyar ba ta sanya ranar gudanar da babban taronta na kasa ba.

Sai dai wasu majiyoyi daga Babban Ofishin Jam’iyyar sun shaida wa Aminiya cewa a watan Maris din ake sa ran gudanar da babban taron.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...