Saurari premier Radio
41.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAn dakatar da zirga-zirga a jihar Zamfara saboda zuwan Buhari

An dakatar da zirga-zirga a jihar Zamfara saboda zuwan Buhari

Date:

A yau Alhamis ne Shugaba Muhammadu Buhari zai sauka a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, a wata ziyarar wuni guda da zai kai.

Tun a jajiberin ziyarar gwamnatin Zamfara ta bayar da sanarwar dakatar da zirga-zirgar ababen hawa ta tsawon sa’a uku a yayin ziyarar ta shugaban Ć™asa.

Gwamnatin jihar dai ta ce shugaban kasar zai je Zamfara ne domin jajanta wa al’ummar jihar game da miyagun hare-haren ‘yan fashin daji na baya-bayan nan musamman a Ć™ananan hukumomin Anka da Bukkuyum.

Kwamishinan YaÉ—a labarai na jihar Zamfara, Malam Ibrahim Magaji Dosara, ya ce tuni suka kammala shirye-shiryen tarbar shugaban kasar.

Ya ce baya ga ta’aziyya da jajen da Shugaba Buhari zai yi wa al’ummar ta Zamfara, zai kuma kara wa sojoji Najeriya da ke jihar kwarin gwiwa a kan irin samame da sauran ayyukan da suke yi wajen fatattakar ‘yan bindigar da ke kai hare-hare a jihar da ma sauran jihohi.

Kwamishinan YaÉ—a labaran ya ce daya daga cikin manufar ziyarar shugaban kasar a Zamfara ita ce domin ya sanyaya zukatan al’ummar ta Zamfara tare da nuna musu cewa yana tare da su.

Malam Ibrahim Dosara ya ce,” Ba jajen Anka da Bukkuyum kadai Shugaba Buhari zai yi ba, zai yi jaje ne ga dukkan iyalan wadanda suka rasa wani nasu a hare-haren ‘yan bindigar a jihar Zamfara”.

A cewarsa a yayin ziyarar shugaban kasar zai gana da jami’an tsaron da ke aiki a jihar da malamai da sarakunan gargajiya da kuma iyalan wadanda suka rasa ransu a yayin hare-haren.

Tuni dai gwamnatin jihar ta bukaci al’ummarta da su kiyaye da dukkan wasu dokoki a yayin ziyarar shugaban kasar.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...