Saurari premier Radio
36.9 C
Kano
Friday, May 17, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiNajeriya Da Birtaniya Sun Kulla Sabuwar Yarjejeniyar Yaki da Safarar Miyagun Kwayoyi.

Najeriya Da Birtaniya Sun Kulla Sabuwar Yarjejeniyar Yaki da Safarar Miyagun Kwayoyi.

Date:

Gwamnatin tarayya da kasar Birtaniya sun sanya hannu kan wata yarjejeniya domin magance matsalar safarar miyagun kwayoyi a wani bangare na kokarin dakile munanan laifuka a kasashen biyu.

An sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar fahimtar junan a Abuja, tsakanin hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA da ta kula da laifukai ta Birtaniya NCA.

Shugaban NDLEA, Buba Marwa ne ya sanya hannun a madadin gwamnatin tarayya yayin da manajan hukumar kula da laifukan kasa ta Birtaniya a yammacin Afirka, David Cater, ya sanya hannu a madadin Birtaniyar.

 

Buba Marwa ya ce wannan sabuwar yarjejeniyar za ta haifar da hanyoyin samun bayanai kan masu aikata laifuka ko inda suke boye don fuskantar hukunci.

A nashi jawabin manajan yammacin Afirka a hukumar kula da laifuka ta Birtaniya, David Cater, ya ce an yi yarjejeniyar ne saboda gamsuwa da ayyukan NDLEA.

 

VON/AH

Latest stories

Related stories