Saurari premier Radio
31.2 C
Kano
Tuesday, April 30, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGobara ta kone shaguna 100 a kasuwar ‘yan katako ta Kaduna

Gobara ta kone shaguna 100 a kasuwar ‘yan katako ta Kaduna

Date:

Wata gobara da ta tashi a Kasuwar Yan Katato da ke karamar hukumar Sabon Garin jihar Kaduna, shaguna 100 da kayayyakin miliyoyin Naira.

Shugaban kasuwar, Mohammed Ashiru, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Zariya cewa, gobarar ta tashi ne sakamakon tartsatsin wayar wutar lantarki da ta bi ta kasuwar.

Ya ce jami’ai sun shawo kan gobarar bayan wasu sa’o’i ta na ci, in da ya jajantawa masu shagunan da abin ya shafa.

Jami’in hukumar kashe gobara ta tarayya, Abubakar Ibrahim, ya ce rashin isassun tafkunan ruwa ne ya jawo tsaikon da aka samu kafin dakatar da ita.

Don haka, ya yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni da su tallafawa wajen samar da rijiyoyin ruwa a yankin.

Latest stories

Ƙungiyar Hamas ta isa birnin Al-Qahira game da tattaunawa kan tsagaita wuta.

Rahotanni daga kasar Masar, sun ce tawagar jami’an kungiyar...

An kashe ƴan ƙato da gora sama da 23 a Barno da Sakkwato.

Rahotanni daga jihohin Borno da Sakkwato sun ce, an...

Related stories