Saurari premier Radio
41.9 C
Kano
Friday, May 3, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiCBN zai sauya fasalin kudaden kasar nan

CBN zai sauya fasalin kudaden kasar nan

Date:

Gwamnan Babban bankin kasa CBN Godwin Emefiele ya ce bankin zai sauya fasalin wasu takardun kuɗin kasar Nan guda uku.

Ya ce babban bankin ya samu amincewar shugaban ƙasar Muhammadu Buhari domin sauya fasalin takartun kuɗi na N200, da N500, da kuma takardar kuɗi ta N1000.

Ya ƙara da cewa sabbin kuɗin za su fara aiki ranar 15 ga watan Disamba da ke tafe.

“Daga yanzu an cire kuɗin da ake karba daga mutane a lokutan da suke zuwa saka kuɗi a banki.

Gwamnan babban bankin ya ƙara da cewa kashi 80 cikin 100 na kuɗaɗen ƙasar nan ana hada-hada da su ne ba ta hanyar bankin ba.

Ya ci gaba da cewa wannan mataki zai ƙara wa kuɗin kasar nan daraja.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...

Related stories