Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabarai'Yan takarar NNPP da PDP basu halarci muhawar takarar gwamna a Kano...

‘Yan takarar NNPP da PDP basu halarci muhawar takarar gwamna a Kano ba

Date:

By Muhammad Bello Dabai

Dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar NNPP, Abba kabir Yusif, da na PDP, Sadiq Wali, basu halarci taron muhawarar ‘yan takarar gwamna da aka gudanar yau a Kano ba.

 

Taron, wanda kungiyar likitoci ta kasa NMA ta shirya, a dakin taro na Otal din Bristol Palace dake jihar Kano, ya maida hankali wajen tattaunawa kan kalubalen da fannin lafiya ke ciki, da kuma hanyoyin magance su.

 

Wadanda suka fafata a muhawarar sun hadar da dan takarar jam’iyyar ADC, Mallam Ibrahim Khalil, da na jam’iyyar LP, Bashir I. Bashir, sai dan takarar jam’iyyar PRP, Salihu Tanko Yakasai, da na APC, Dr Nasiru Yusif Gawuna, sai kuma na jam’iyyar ADP, Sha’aban Ibrahim Sharada, wanda ya sami wakilcin mataimakinsa.

 

Da yake zantawa da Premier Radio, shugaban kungiyar likitocin ta kasa NMA, reshen jihar Kano, Abdullahi Sulaiman, ya ce makasudin shirya muhawarar shi ne bawa ‘yan takarar damar bayyana kudiransu a bangaren lafiya, da kuma saukakawa al’umma yin alkalanci, wajen zaben na gari.

 

Inda Kowanne Dan Takara Yafi Maida Hankali

 

Yayin muhawarar, wadda ta gudana a zagaye 3, bisa mabanbantan tambayoyi, an nemi jin ta bakin yan takarar kan tsarin da suke da shi na farfado da harkokin kiwon lafiya, ta hanyar magance kalubalen da fannin ke fuskanta.

 

A jawabin sa, dan takarar jam’iyyar ADC, Mallam Ibrahim Khalil, ya hakikance cewa rashin tabbatar da doka da oda, itace kashin bayan tabarbarewar harkar lafiyar, dama sauran fannoni.

Yace matukar ana son ganin daidai, wajibi ne a tabbatar da doka, musamman ta hanyar hukunta masu yi mata karan tsaye, ba tare da nuna banbanci ba.

Mallam Khalil, wanda shahararren malamin addinin musulunci ne, ya ce ta hanyar samar da sahihin shugabanci, cimma wannan kudiri abu ne mai sauki.

 

To sai dai a nasa jawabin, dan takarar jam’iyyar APC, wanda sh ine mataimakin gwamnan Kano mai ci, Dr Nasiru Yusuf Gawuna, yace duk gwamnatin da zata zo a nan gaba, bata bukatar yin kari kan hidimar da suka yi wa fannin lafiyar, illa kawai tattala abinda aka gina.

 

Ya bayyana kudirinsa na dorawa daga inda gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tsaya, yana mai nuna gamsuwa da halin da fannin ke ciki a jihar Kano a halin yanzu.

 

A nasa bangaren, dan takarar gwamna a jam’iyyar ADP, Sha’aban Ibrahim Sharada, wanda ya sami wakilcin mataimakinsa, Rabi’u Sulaiman Bako, yace hanya mafi sauki ta magance matsalolin fannin lafiyar shine, hada kai da kungiyoyin kasa da kasa, domin shiryawa ma’aikatan lafiyar horo, baya ga kula da walwalarsu.

Yace tuni suka sami ganawa da kwararru daga kasashen Asia da na Turai wajen tsara yadda za’a tunkari batun.

 

Shi kuwa, dan takarar gwamna a jam’iyyar Labour Party, Bashir Ishaq Bashir, cewa yayi, ba wait sari da dokoki ne babu a fannin lafiyar ba, babban kalubalen shine wanzar da su.

Yana ganin ta hanyar tabbatar da duk tsarikan da aka samar, za’a iya cimma kyakkyawan cigaba, inda ya bada misali da wasu tsare tsare da gwamnatin Kano ta kawo, kuma kawo yanzu ba’a kai ga aiwatar wa ba.

 

Dan takarar jam’iyyar PRP, Salihu Tanko Yakasai kuwa, cewa yayi bijiro da sabbin tsare tsare, wadanda zasu karbi shirin sauyin da ake fatan tabbatarwa, itace hanyar da zai bi wajen inganta fannin na lafiya.

 

Yace samar da tsarin lafiya kyauta ga marasa karfi, da kuma kulawa da walwalar ma’aikata, musamman ta fuskar smar da masu da kayan aiki da wadataccen kudi, na daga cikin abinda zai mayar da hankali.

 

Halin Da Bangaren Lafiya Ke Ciki a Jihar Kano

 

Cikin jimillar kwararrun likitoci 1,063 dake akwai a jihar Kano, guda 533 ne kacal ke karbar albashi, yayinda ragowar ke aikin sa kai.

 

Daga cikin su, akwai likitoci 400 dake aiki a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano, sai guda 96 a Asibitin Kashi na Dala, sannan ragowar 84 dake aiki a asibitocin kudi daban daban dake jihar.

 

Shugaban kungiyar likitocin ta kasa reshen jihar Kano, Kabir Sulaiman ne ya bayyana alkaluman ga yan jarida, a wajen taron muhawarar yan takarar gwamnan da aka gudanar.

 

Wannan ke kara fito da girman kalubalen da fannin lafiya a jihar Kanon ke ciki, musamman a yankunan karkara, a gabar da kwararrun likitoci ke kara kwarara kasashen ketare domin yin aiki a can.

 

Ko da a yan watannin baya, kimanin likitoci 200 ne suka sami lasisin aiki a Burtaniya, wanda ya kai jimillar adadin yan asalin Najeriya dake aiki a kasar da sama da mutum dubu 10.

 

Yawancin su na alakanta ficewar ce da rashin kyakkyawan yanayin aiki a Najeriya, kama daga rashin albashi mai kyau, zuwa rike kudin alawus da kuma rashin wadatattun kayan aiki.

 

Abinda Ake Sa Ran Ya Biyo Bayan Muhawarar

 

Kamar yadda shugaban kungiyar likitocin ta kasa NMA reshen jihar Kano, Abdullahi Sulaiman ya bayyana, makasudin shirya muhawarar itace bawa yan takarar gwamna a Kano damar bayyana tsarin da kowannen su ke fatan bijiro das hi, domin ceto fannin lafiyar jihar daga halin da yake ciki.

 

Ana fatan wannan muhawarar, zata haskawa al’umma inda kowanne dan takara ya sanya gaba domin yin alkalanci.

 

Makamanciyar wannan muhawara na matukar tasiri wajen zaben shugaba a kasashen da suka ci gaba, inda jama’a ke la’akari da kyawun manufar da takara, ba wai yanki, kabila, yare ko addini ba.

 

Kamar yadda masharanta suka sha fada, billowar irin wannan tsari a Najeriya, alama ce dake nuna cigaba da dimokradiyyar kasar ta samu.

 

A shekarar 2023 ne za’a gudanar da zaben shugaban kasa da na gwamnoni, day an majalisun tarayya da na jihohi, kuma sakamakon sa ne zai zamo ma’auni kan inda kasar zata sanya gaba

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories