Saurari premier Radio
23.9 C
Kano
Saturday, February 24, 2024
Saurari Premier Radio
HomeAl'aduDr Mansur Mukhtar Adnan ya zama sabon sarkin Ban Kano

Dr Mansur Mukhtar Adnan ya zama sabon sarkin Ban Kano

Date:

Da safiyar ranar juma’ar nan 28 ga Oktoban Shekarar 2022 aka nada Dr Mansur Mukhtar Adnan a matsayin sabon Sarkin Ban Kano na Tara a tarihin Masarautar Kano.

 

Nadin Sabon Sarkin Ban Kanon dai ya gudana a fadar masarutar Kano a wannan rana ta Juma’a.

 

Dr Mansur Mukhtar Adnan ya maye gurbin mahaifinsa Alhaji Mukhtar Adnan wanda ya rasu yana da shekara 95, Bayan rashin lafiya da yayi fama da ita.

 

Bikin nadin sabon Sarkin ban dai ya samu halartar Karamin ministan ayyyuka na kasa Umar El Yakub da Mataimain gwamnan Kano Nasir Yusuf Gawuna.

 

Haka zalika shima Shugaban Majalisar dokokin jihar Kano da kuma mataimakin dan takarar gwamnan Kano a jami’iyyar NNPP Aminu Abdussalam sun halarci nadin.

 

Haka Kuma bikin nadin ya samu halartar baki daga sassan daban-daban na jihohin kasar na.

 

Haka zalika an kuma nada Alhaji Bashir Mahe sabon walin Kano, wanda Shima aka gudanar bikin nadin nasa a wannan rana ta Juma’a a fadar Masarautar Kano.

Latest stories

Related stories