Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Monday, April 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiCBN Basu tuntube ni ba game da chanja takardar kudi- Zainab Ahmad

CBN Basu tuntube ni ba game da chanja takardar kudi- Zainab Ahmad

Date:

Faisal Abdullahi Bila

 

Ministar kudi, kasafi da tsare tsaren kasar nan Zainab Ahmad ta ce bankin kasar bai nemi shawarar ta ba kan chanja takardar kudi, sai jin labarin shirin ta yi a kafafen yada labarai.

 

Zainab Ahmad na wanann batu ne lokacin da take kare kasafin kudin ma’aikatar ta na shekarar 2023.

 

Ministar Kudin ta kuma gargadi Gwamnan bankin kasa CBN kan shirin da yake na sauya tsarin takardar kudi.

Tace yin hakan zai zubar da darajar naira a kasashen duniya.

 

A cewar ta “ba a wannan lokacin ya dace a yi maganar sauya tsarin takardar kudin kasar nan ba”

 

A ranar Larabar nan ne gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ya sanar da shirin sauya tsarin takardar kudi ta naira 200, naira 500 da kuma naira 1000 da nufin kawo cigaba a harkar kudin kasar nan.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories