Saurari premier Radio
37.9 C
Kano
Friday, May 17, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiCBN na da damar canja Nera ba tare da tuntubar kowa ba...

CBN na da damar canja Nera ba tare da tuntubar kowa ba – Emefiele

Date:

Hafsat Iliyasu Dambo

 

Babban Bankin Najeriya CBN ya ce ya bi doka da ka’ida wajen sauya fasalin takardun kudin kasar uku da yake shirin yi.

 

 

Kakakin CBN, Mista Osita Nwanisobi, na mayar da martani ne ga Ministar Kudi Zainab Shamsuna Ahmed, wadda ta ce ba a tuntubi ma’aikatarta ba kafin aiwatar da sauyin.

 

 

Da take jawabi lokacin da ta bayyana a gaban wani kwamatin Majasliar Dattawa ranar Juma’a, Zainab ta soki shirin tana mai cewa ba lokacin da ya dace ba ne.

 

 

Sai dai Mista Nwanisobi ya ce hukumomin CBN sun bi ka’ida wajen neman amincewar Shugaba Buhari kamar yadda sashe na 2(b) da sashe na 18(a) da sashe na 19(a) (b) na dokar CBN ta 2007 suka tanada don neman sauya fasali, fara aiki da kuma yada sabbin takardun kudi na N200 da N500 da N1,000.

 

 

Idan za’a iya tunawa a ranar Laraba ne babban bankin ya ba da sanarwar sake takardun na naira, inda ya ce kashi 80 cikin 100 na kudaden kasar na hannun mutane maimakon bankunan kasuwanci.

 

CBN ya bai wa ‘yan kasar wa’adin kwana 42 da su mayar da kudade ga bankunan kasuwanci kuma yana sa ran nan da 15 ga watan Disamba mai zuwa zai fitar da sabbin takardun N200 da N500 da N1,000.

Latest stories

Related stories