Saurari premier Radio
37.5 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin Tarayya za ta fitar da ‘Yan Najeriya miliyan 100 daga kangin...

Gwamnatin Tarayya za ta fitar da ‘Yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci – Minista

Date:

Ministan Sufuri, Mu’azu Sambo, ya ce gwamnatin tarayya na shirin samar da ayyukan yi ga mutane miliyan 21 tare da fitar da mutane miliyan 35 daga kangin talauci nan da shekarar 2025.

 

Sambo, a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Dr Sam Idiagbonya, ya fitar ya bayyana hakan a ranar Juma’a a taron da ake yi na ministoci a Uyo, Akwa Ibom.

 

A cewarsa, fannin sufurin na shirin cimma kudurin gwamnati na fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci a cikin shekaru 10.

 

Sambo ya ce gibin ababen more rayuwa da ake samu a fannin ya sa ba a samun ci gaba a fannin, hakan yasa suka fitar da sabon tsarin ci gaba na matsakaicin lokaci 2021-2025 da Tsari mai tsayi mai suna Nigeria Agenda 2050.

 

Tsarin zai bada damar sanya hannun jari mai yawa a cikin ababen more rayuwa, inganta tattalin arziki, inganta yanayin rayuwa da aiwatar da rage sauyin yanayi.

 

Hakan zai samar da ayyukan yi ga mutum miliyan 21 da kuma fitar da mutane miliyan 35 daga kangin talauci nan da shekara ta 2025, ta yadda za a kai ga cimma burin gwamnati na fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci a cikin shekaru 10.

Latest stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...

Related stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...