Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDamfarar Dala Miliyan 1.3: A A Zaura ya yi batan dabo

Damfarar Dala Miliyan 1.3: A A Zaura ya yi batan dabo

Date:

Dan takarar sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC Abdulkarim A Zaura ya yi batan dabo bayan da hukumar EFCC ta gurfanar da shi gaban kotu kan zargin almundahanar kudade.

 

Hukumar ta EFCC ta shaidawa babbar kotun tarayya da ke nan Kano a zamanta na ranar Litinin cewar ta nemi AA Zaura kasa ko sama ta rasa.

 

Hukumar ta EFCC dai ta gurfanar da shi ne kan zargin mallakar kudaden da suka Kai Dala 1,300,000 ba bisa ka’ida ba.

 

A cewar lauyar EFCC Aisha Habib, wanda ake kara ba za a iya gurfanar da shi a gaban kotu raayal aini ba saboda yayi batan dabo.

 

A cewarta laifin babbane da ya zama dole wanda ake kara ya bayyana a gaban kotu don amsa tuhamar da ake yi masa.

 

“Idan ma yana jin cewa kotun ba ta da hurumin da za ta saurari karar ya zama dole ya bayyana gabanta kafin ya kalubalanceta”

 

“Wannan rashin girmama kotu ne, dole ne ya bayyana a gabanta kafin ya ce zai kalubalanci hurumin kotun” A cewarta.

 

Sai dai lauyan na A A Zaura Ibrahim Garba Waru, ya ce a halin da ake ciki bayyanar wanda ake Kara bashi ne abin damuwa ba.

 

A cewarsa wanda ake kara ya gaza bayyana a kotu saboda rashin lafiya da ke damunsa.

 

Anasa bangaren mai shari’a Muhammad Nasir ya ce a irin wanna shari’ar ta damfara ya zama dole wanda ake kara ya bayyana a gaban kotu.

 

A don hakan ne ya bukaci abi dukkan matakan shari’a a kuma tabbatar ya bayyana a gaban kotun.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories