Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMajalisar Kano ta sake tantance sabon kwamishina

Majalisar Kano ta sake tantance sabon kwamishina

Date:

Majalisar dokokin Kano ta amince da nadin Kabiru Muhammad Tarauni, a matsayin kwamishina kuma dan majalisar zartaswa na jihar Kano.

 

Majalisar ta amince da shine a zamanta na Litinin din nan karkashin shugabanta Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari.

 

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ne ya aike sa sunan sa ga majalisar dokokin domin tangancewa tare da amincewa dashi a matsayin kwamishina.

Majalisar dokokin Kano zata binciki ambaliyar ruwan kasuwar Kantin Kwari

A yanzu dai shine mutum na goma sha daya da majalisar ta amince domin nada su a matsayin kwamishinoni da zasu maye gurbin wadanda suka ajiye aiki don yin takara a zaben badi dake tafe.

 

Kafin amincewa dashi Kabiru Muhammad Tarauni, ya taba zama dan majalisar dokokin Kano karo biyu daga shekarar 2003 zuwa 2011.

 

Yayin zaman sa a majalisar ya rike mukamin bulaliyar majalisa.

 

Haka zalika ana ganin sa a matsayin daya daga cikin manyan magoya bayan tsohon kwamishinan kananan hukumomi zamanin gwamnatin Ibrahim Shekarau, wato Malam Salihu Sagir Takai.

 

Yayin tantance shi dai Kabiru Muhammad Tarauni ya samu rakiyar mutane da dama ciki harda tsohon kwamishinan ilimi Farouk Iya da Salihu Sagir Takai da shugaban karamar hukumar tarauni da dai sauransu.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...