Saurari premier Radio
36 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMajalisar dokokin Kano zata binciki ambaliyar ruwan kasuwar Kantin Kwari

Majalisar dokokin Kano zata binciki ambaliyar ruwan kasuwar Kantin Kwari

Date:

Majalisar dokokin Kano ta kafa kwamiti da zai binciki ambaliyar ruwa da rugujewar gidaje da ake samu a wasu daga cikin kasuwanni da yankunan jihar nan baki daya.

 

Majalisar karkashin shugabanta Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ta kafa kwamitin ne yayin zamanta na Litinin din nan.

 

Tunda fari dai dan majalisa mai wakiltar Fagge Muhammad Tukur, ne ya gabatar da gudurin gaggawa dake neman majalisar tayi bincike kan musababin ambaliyar ruwan da kasuwar Kantin Kwari, ke fuskanta a damunar bana tare da tallafawa wadanda iftila’in ya shafa.

 

Sai dai bayan tattaunawa da akayi majalisa ta amince kudurin ya hada da sauran kasuwanni da guraren da ambaliyar ruwan ta shafa a ciki da wajen kananan hukumomin jihar nan.
Ga Karin bayanin da dan majalisar mai wakiltar Fagge, Tukur Muhammad, yayi mana kan kudurin.

 

Ambaliyar ruwa na ci gaba da rusa gidaje a Kano

 

Tuni dai majalisar ta baiwa shugaban kwamitin bada agajin gaggawa na majalisar Aminu Sa’ad Ungoggo, ya jagoranci kwamitin ayyuka dana muhalli tare da gabatar da rahoton su nan da makwanni biyu domin daukar mataki akai.

 

Sai dai kan wannan mun tuntubi kwamishinan muhalli Kabiru Ibrahim Getso, inda yace gine-gine da akeyi akan magudanan ruwa ne ya haddasa ambaliyar ruwa a kasuwar Kantin Kwari da sauran kasuwannin jihar nan.

 

Kabiru Ibrahim Getso, ya ce gwamnati tana yin nata kokarin don magance matsalar don haka akwai bukatar al’umma su bata hadin kai wajen yashe magudanan ruwa tare da zubar da shara a inda gwamnati ta tanadar a yankunan su.

Latest stories

Related stories