Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Thursday, May 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiINEC ta ja kunnen jam'iyyu kan jinkirta zaben fidda gwani

INEC ta ja kunnen jam’iyyu kan jinkirta zaben fidda gwani

Date:

Mukhtar Yahya Usman
Hukumar zabe ta kasa INEC ta ce ba za ta daga kafa ga duk jam’iyyar da ta gaza fitar da dan takarar a zaben fidda gwani ba, cikin wa’adin da ta bayar.

Daraktan yada labaran hukumar Festus Okoye ne ya bayyana hakan ranar Alhamis.

Ya ce tun a ranar 26 ga watan Fabarairu aka gabatar da shirin zaben shekarar 2023 da ya umurci jam’iyyun da su gudanar da zaben fidda gwani tsakanin ranakun 4 ga watan Afrilu zuwa 3 ga watan Yunin wannan shekara.

Okoye ya ce bisa wannan jadawali, duk wani zaben fidda gwanin da akayi bayan wadannan ranaku ya zama haramtacce, kuma hukumar ba za ta amince da shi ba.

Daraktan yace sun shaidawa daukacin Jam‘iyyu 18 dake da rajista wannan doka kamar yadda Sashe na 82 na Dokar Zaben shekarar 2022 ya tanada.

Okoye yace tuni wasu daga cikin jam’iyyun suka fara shirin aiki da dokar, kuma hukumar zabe ta tura jami’an ta domin sanya ido akan yadda suke gudanar da zaben.

Idan dai ba’a manta ba, sabawa dokar zabe wajen gudanar da zaben fidda gwani ya sa Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara ta rasa kujerar gwamna da Yan majalisun tarayya da na jiha a zaben shekarar 2019.

Latest stories

Related stories