Saurari premier Radio
31.2 C
Kano
Tuesday, April 30, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiTallafin mai:Buhari ya nemi majalisa ta kara tiriliyan 2.5 cikin kasafin kudi

Tallafin mai:Buhari ya nemi majalisa ta kara tiriliyan 2.5 cikin kasafin kudi

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika wa Majalisun Dokokin Kasar nan bukatar kara Naira Tiriliyan 2.557 a Kasafin Kudin 2022 domin biyan tallafin man fetur.

Premier Radio ta ruwaito fadar gwamnatin tarayya ta mika wa majalisun tarayyar bukatar ne a ranar Talata domin tarar hanzarin biyan tallafi man fetur da aka yanke shawarar ci gaba da biyan dillalan man fetur.

Bukatar neman gyaran ya biyo bayan dakatar da dokar nan fetur (PIA) ce, wadda ta tanadi a soke biyan tallafin man fetur din da kuma mayar da hada-hadar mai ta ’yan kasuwa zalla.

Wannan na kunshe ne cikin wata wasika da shugaban ya rubuta wa ’yan majalisar wadda kuma Shugaban Majalisa Sanata Ahmad Lawan da Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila suka karanta a zaurukan majalisunsu.

A halin yanzu dai gwamnati na neman majalisar ta amince da karin fiye da naira tiriliyan biyu da rabi (triliyan N2.557) don biyan kudin tallafin mai daga Yuli zuwa Disamban 2022 da kuma sake duba Dokar Kudi ta Finance Act 2021.

A cikin wasikar, Buhari ya ce gyaran ya zama dole don kara wasu ayyuka a ciki da suka hada da tallafin man fetur, wanda tun farko gwamnatinsa ta yi niyyar daina biya kafin daga baya ta sauya shawara.

Tun da farko gwamnati ta tanadi kudin tallafin na wata shidan farko na shekarar 2022 a kasafin kudin, inda aka ware biliyan N443 daga Janairu zuwa Yunin 2022.

Latest stories

Ƙungiyar Hamas ta isa birnin Al-Qahira game da tattaunawa kan tsagaita wuta.

Rahotanni daga kasar Masar, sun ce tawagar jami’an kungiyar...

An kashe ƴan ƙato da gora sama da 23 a Barno da Sakkwato.

Rahotanni daga jihohin Borno da Sakkwato sun ce, an...

Related stories

Ƙungiyar Hamas ta isa birnin Al-Qahira game da tattaunawa kan tsagaita wuta.

Rahotanni daga kasar Masar, sun ce tawagar jami’an kungiyar...

An kashe ƴan ƙato da gora sama da 23 a Barno da Sakkwato.

Rahotanni daga jihohin Borno da Sakkwato sun ce, an...