Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Saturday, April 20, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKotu ta daure kishiyoyi biyu saboda cizon juna

Kotu ta daure kishiyoyi biyu saboda cizon juna

Date:

Wata kotun shari’ar musunlunci da ke Rigasa a Jihar Kaduna, ta daure wasu matan aure biyu saboda ba wa hammata iskar da suka yi.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Salisu Abubakar Tureta, ne ya zartar musu da hukuncin daurin sati biyu a gidan gyaran hali, bayan gano matan biyu sun dambata tare da cizon juna.

Abubakar Tureta, ya ce daurin wani hukunci ne da zai koya musu hankali da kaunar zaman lafiya a tsakaninsu.

Daya daga cikin matan, Azima Usman Tasiu, ce ta shigar da karar kishiyarta, Aisha Tasi’u a gaban kotun kan zargin cizonta.

Azima, ta shaida wa kotun cewar ita ce mata ta uku ga Tasi’u, inda ta kara da cewar kishiyarta ta mata dukan tsiya bayan samun sabani tsakaninta da yaron A’isha.

Sai dai wadda ake tuhumar (A’isha), ta ce Azima ce ta fara takalarta da neman fada sannan kuma ta cije ta a kafada.

Ko da kotun ta bukaci mijin nasu Tasi’u, ya bayar da ba’asin abin da ya faru, sai ya kada baki ya ce ya tarar da su suna fada ne, bai san abin da ya hada su ba.

Tasi’u, ya ce duk hukuncin da kotun ta yanke musu a ranar 28 ga watan Fabrairu, zai iya sa wa ya sauwake musu baki daya.

Latest stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Related stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...