
Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zullum ya ce, gwamnati da jami’an tsaro na ƙoƙarin ceto daliban makaranta da aka sace a makarantar firamare a ƙauyen Mussa dake ƙaramar Hukumar Askira- Uba.
Gwamna Zulum ya bayyana haka ne ya yin wata ziyarar jaje da ya kai Askira Uba dangane da iftila’in da ake dangantawa da Boko Haram.
Shirin AGILE zai dauki dalibai dubu 50 a kanannan hukumomin Kano 44
Ziyarar na zuwa ne yayin da aka shiga kwanaki na 5 da sace daliban ciki harda kanan yara.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da samun nasara dakile satar motoci.
Kawo yanzu dai, babu wani cikakken rahoton inda yaran suke, wanda ya sanya iyayensu cikin dimuwa da tashin hankali
