Jami’an Hukumar Hisba ta Jihar Kebbi sun cafke wani mutum da ake zargin an same shi a boye cikin buhun “Ghana Must-Go” a gidan wata matar aure da ke unguwar Badariya a Birnin Kebbi.
Darakta mai kula da harkokin Shari’a na hukumar, Sirajo Kamba, ne ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
A cewarsa, mazauna unguwar sun sanar da jami’an Hisba da misalin ƙarfe 12:15 na dare bayan sun ga mutumin ya shiga gidan matar cikin yanayi da ya jawo zargi.
