Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana tsohon shugaban ƙasa Janar Yakubu Gowon a matsayin abin koyi ta fuskar nagarta, gaskiya da kishin ƙasa.
Sarkin ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da littafin rayuwar tsohon shugaban ƙasar a birnin tarayya Abuja, inda ya ce kyakkyawan tarihi da ɗabi’a sune abubuwan da suka fi dawwama a rayuwar shugabanni.
Muhammadu Sanusi II ya ce abin da ya fi kasancewa a tarihin shugabanci ba gine-gine ko manufofi ba ne, sai dai nagarta da kyakkyawan shugabanci, yana mai cewa waɗannan abubuwa kan kasance abin tunawa ga al’umma na dogon lokaci.
Ya kuma bayyana tsohuwar alakar da ke tsakaninsu da Janar Yakubu Gowon tun daga zamanin mahaifinsa, inda ya ce Gowon ya taɓa naɗa mahaifinsa a matsayin jakada a ƙasashe daban-daban.
Wakilinmu Khalil Ibrahim Yaro ya ruwaito cewa, taron ya samu halartar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, da Janar Abdulsalami Abubakar tare da sauran manyan baƙi.
