Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun yi garkuwa da wata malamar makarantar firamare, Amina Hussaini, a gidanta da ke garin Kuru, a Ƙaramar Hukumar Toto ta Jihar Nasarawa, inda suka nemi kuɗin fansa naira miliyan 50 domin sakinta.
Wata ƴar uwar malamar, Suwaiba Abdullahi, ce ta tabbatar da faruwar lamarin yayin zantawarta da jaridar Daily Trust a ranar Alhamis.
A cewarta, maharan sun sace Amina ne a ranar Talata, lokacin da mijinta ya tafi birnin Lafia domin gudanar da wani aiki.
Suwaiba ta bayyana cewa masu garkuwar sun buƙaci a biya naira miliyan 50 kafin su saki malamar.
Ta ƙara da cewa har yanzu Amina na hannun waɗanda suka sace ta, yayin da iyalanta ke cikin damuwa kan halin da take ciki.
Haka kuma, ta tabbatar da cewa an kai rahoton lamarin ga rundunar ƴan sandan jihar domin ɗaukar matakan da suka dace.
Sai dai kawo yanzu, babu wani ƙarin bayani daga rundunar ƴan sandan Jihar Nasarawa kan matakan da take ɗauka domin kuɓutar da malamar.
