Rundunar ƴan sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da kuɓutar da limaman addinin Musulunci uku daga cikin shida da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a watan Satumban 2026.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, Muhammad Bello, ya bayyana cewa an kuɓutar da limaman ne sakamakon haɗin gwiwar jami’an tsaro, ciki har da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da Ofishin Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro.
A cewarsa, an sace limaman ne a ranar 12 ga Satumba, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Talata Mafara domin halartar wata addu’a ta musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Kwamishinan ya ce limaman ukun da aka kuɓutar suna cikin ƙoshin lafiya, bayan da aka duba lafiyarsu.
Ya ƙara da cewa jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da ayyukan ceto domin kuɓutar da sauran limamai uku da har yanzu suke hannun masu garkuwa da mutane.
Rundunar ta jaddada cewa tana ci gaba da haɗa kai da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da kuɓutar da sauran waɗanda aka sace.
