Hukumar Hisbah ta Ƙaramar Hukumar Birni a Jihar Kano ta kama wani mutum mai suna Ishaku Musa, bisa zargin safarar naman kare da barasa daga kasuwar Sabon Gari zuwa unguwar Fanshekara.
Jami’an hukumar sun kama wanda ake zargin ne a yankin Dorayi Caranci, bayan samun bayanan sirri kan kayayyakin da ake zargin yana ɗauke da su.
Kwamandan Hisbah na ƙaramar hukumar, Hamidan Tanko Alasaka, ya bayyana cewa hukumar ta fara gudanar da bincike kan lamarin domin gano cikakkun bayanai.
Ya ce bayan kammala binciken, hukumar za ta ɗauki matakan gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bisa tanadin doka.
Kwamandan ya kuma buƙaci al’umma da su ci gaba da bai wa hukumar haɗin kai ta hanyar kai rahoton duk wasu ayyuka da ake zargin sun saɓa wa doka.
A cewarsa, haɗin kan jama’a da jami’an Hisbah zai taimaka wajen inganta ayyukan hukumar da tabbatar da bin doka a jihar.
