Rundunar ƴan sandan Jihar Jigawa ta kama wani matashi mai suna Emmanuel, mai shekaru 29, bisa zargin kashe Ibrahim Shago, mai shekaru 32, sakamakon wata saɓani da ya shiga tsakaninsu a garin Dutse.
Kakakin rundunar, SP Shi’isu Adam, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, 30 ga Oktoba, 2026.
A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:45 na yammacin ranar Alhamis, 29 ga Oktoba, a yankin Rafin Sanyi da ke Ƙaramar Hukumar Dutse.
Rundunar ta bayyana cewa wanda ake zargin, mai sana’ar aski a Moonlight Hotel da ke yankin, ya daba wa Ibrahim Shago wuƙa a wuya bayan wata takaddama da ta shiga tsakaninsu.
Ƴan sandan sun kuma ce ana zargin matashin yana cikin maye a lokacin da lamarin ya faru.
An garzaya da Ibrahim Shago zuwa asibiti domin samun kulawar gaggawa, sai dai daga bisani likita ya tabbatar da rasuwarsa.
Bayan faruwar lamarin, wasu fusatattun matasa sun yi yunƙurin lalata otal ɗin da abin ya faru a kusa da shi, amma jami’an ƴan sanda suka shiga tsakani tare da shawo kan lamarin.
Rundunar ta tabbatar da cewa wanda ake zargin yana hannunta, yayin da ake ci gaba da bincike domin gurfanar da shi a gaban kotu.
Kwamishinan ƴan sandan Jihar Jigawa, CP Tijjani Murtala, ya yi kira ga al’umma da su guji ɗaukar doka a hannunsu, tare da barin hukumomin tsaro su gudanar da aikinsu bisa tanadin doka.
