Hukumar Tsaron Farin Kaya (NSCDC) reshen Jihar Kano ta rufe wani wurin tace man dizal da ake zargin yana gudanar da ayyukansa ba bisa ƙa’ida ba a yankin Panisau da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo, tare da kama mutum biyar.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya fitar a ranar Juma’a.
Sanarwar ta bayyana cewa an kama mutanen ne bisa zargin gudanar da harkokin man fetur da iskar gas ba tare da rajista ko izinin hukumomin da abin ya shafa ba.
Waɗanda aka kama sun haɗa da Ibrahim Bello mai shekaru 28, Musbahu Adam mai shekaru 38, Rabiu Dahiru mai shekaru 27, Haruna Kabiru mai shekaru 26 da Sunusi Ahmad mai shekaru 25.
Kwamandan hukumar NSCDC na Jihar Kano, Hassan Mohammed Agalama, ya buƙaci al’umma da su riƙa kai rahoton duk wani aiki da ake zargin ana gudanar da shi ba bisa ƙa’ida ba ga hukumomin tsaro.
Ya jaddada muhimmancin haɗin kan jama’a da jami’an tsaro wajen daƙile ayyukan da ka iya jefa rayuka da dukiyoyin al’umma cikin haɗari.
