Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Afirka (Africa CDC) ta bayyana damuwa kan yadda cutar Ebola ke ci gaba da yaɗuwa a wasu ƙasashen nahiyar, duk da matakan da hukumomin lafiya ke ɗauka domin shawo kanta.
Shugaban hukumar, Dr. Jean Kaseya, ya bayyana cewa an samu sama da mutum dubu 10 da suka kamu da cutar, yayin da adadin waɗanda suka mutu ke kusantar dubu biyar.
Bayanan hukumomin lafiya sun nuna cewa Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ce ta fi fama da cutar, inda aka samu mafi yawan masu kamuwa da ita da kuma mace-mace.
A ƙasar Kenya kuwa, an tabbatar da mutum tara da suka kamu da cutar, yayin da biyu daga cikinsu suka rasu.
A Najeriya kuma, Hukumar NCDC ta tabbatar da bullar cutar a ranar 20 ga Oktoba, 2026, bayan gwajin wata mata mai shekaru 42 da ta dawo Abuja daga Uganda ya nuna tana ɗauke da cutar.
Bayan samun kulawar likitoci da daidaituwar yanayin lafiyarta, an kwashe matar zuwa Switzerland a ranar 26 ga Oktoba domin ci gaba da jinya.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa, duk da cewa babu wanda aka sani yana ɗauke da cutar a Najeriya bayan fitar matar, hakan ba yana nufin an kawo ƙarshen matakan sa ido da rigakafin cutar ba.
Hukumomin lafiya sun ci gaba da bin diddigin mutanen da suka yi mu’amala da matar, domin tabbatar da cewa cutar ba ta sake yaɗuwa ba.
