Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana sunayen jami’an da ke da hannu wajen shigar da hotunan da aka ƙirƙira ta amfani da fasahar basirar wucin gadi (AI) cikin rajistar masu zaɓe.
Atiku ya bayyana damuwa kan bayanan da aka danganta ga hukumar INEC, waɗanda suka nuna cewa an gano wasu hotunan AI da kura-kurai a cikin rajistar masu zaɓe.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce irin wannan matsala na iya haifar da shakku kan sahihancin rajistar masu zaɓe, musamman yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.
Ya buƙaci hukumar ta gudanar da bincike mai zaman kansa domin gano yadda aka shigar da hotunan, tare da bayyana sakamakon binciken ga al’umma.
Atiku ya kuma yi kira da a ɗauki matakin da doka ta tanada kan duk jami’in da bincike ya tabbatar yana da hannu wajen aikata ba daidai ba.
A cewarsa, bai kamata hukumar INEC ta tsaya ga amincewa da samun kura-kurai a rajistar ba, ba tare da bayyana cikakken bayani kan musabbabin matsalar da matakan da take ɗauka domin magance ta ba.
Ya kuma yi kira ga jam’iyyun adawa da ƙasashen duniya da su sanya ido kan yadda hukumar za ta magance lamarin, domin tabbatar da gaskiya da amincin zaɓen 2027.
Atiku ya yi gargaɗin cewa rashin warware matsalar yadda ya kamata na iya raunana amincewar jama’a da tsarin zaɓen Najeriya.
