kungiyar ƴan kasuwar shinkafa ta Kwanar Dawaki da ke Jihar Kano ta yi kira ga mambobinta da masu sayen shinkafar da aka fi sani da Fadi da su dakatar da saye da sayar da ita na ɗan lokaci, sakamakon sauye-sauyen farashi da ake samu a kasuwa.
Ƙungiyar ta bayyana cewa rashin daidaiton farashin shinkafar na jefa ƴan kasuwa cikin asara, musamman waɗanda ke sayen kaya da tsada, amma daga bisani farashinsa ya sauka kafin su sayar.
A cikin wata sanarwa da hukumar kasuwar ta fitar, ta ce dakatar da hada-hadar shinkafar na ɗan lokaci zai taimaka wajen rage asarar da ƴan kasuwa ke fuskanta, tare da ba da damar farashin ya daidaita.
Shugaban ƙungiyar, Sham’unu Salihu Nasiru, ya buƙaci mambobinta da su yi la’akari da halin da kasuwar ke ciki, tare da bin shawarar har zuwa lokacin da za a samu daidaiton farashi.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana takamaiman lokacin da ake sa ran ci gaba da hada-hadar shinkafar ba.
